Muhimmancin Artificial Intelligence (AI) a Duniyar Yau
Gabatarwa A yau duniya tana canzawa cikin sauri sakamakon ci gaban fasaha. Daga wayoyin hannu zuwa kwamfuta, daga intanet zuwa manhajojin zamani, fasaha ta zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan Adam. Daya daga cikin manyan ci gaban da ake magana akai sosai a wannan zamani shi ne Artificial Intelligence (AI), wato na’ura mai kwaikwayon tunani ko basirar ɗan Adam. Artificial Intelligence wata fasaha ce da ake ƙirƙira domin na’ura ko kwamfuta ta iya yin wasu ayyuka da a da sai mutum ne kawai zai iya yi, kamar tunani, nazari, tantance bayanai, fahimtar magana, bada amsa, ko yanke shawara. A takaice, AI na taimaka wa na’ura ta yi aiki cikin basira fiye da yadda aka saba. A wannan zamani, AI ya shiga kusan kowane fanni na rayuwa. Ana amfani da shi a makarantu, asibitoci, bankuna, kasuwanci, sadarwa, tsaro, da ma kafafen sada zumunta. Wasu mutane suna amfani da shi ba tare da sun sani ba, musamman idan suna amfani da wayar hannu, Google, YouTube, ko wasu apps na zamani. A wannan article, ...